Wednesday, January 15
Shadow

Mun samu nasarar fara haƙo ɗanyen mai ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas a rana – NNPCL

Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya ce ya samu nasarar kai ga haƙo ɗanyen mai ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas a kowacce rana.

Shugaban Kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da ya gudana a Abuja.

Ya ce alƙaluman da aka samu sun haɗa daga watan Yuni zuwa Nuwamban da muke ciki.

Kamfanin wanda cikin shekaru 15 da suka gabata ya yi ta fama da rashin taron na masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan harkokin kasuwancin masu zuba jari kuma hakan ya ja raguwar yawan gangar man da yake samarwa a kowacce rana.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wani mutum ya lakadawa 'yansandan Najeriya biyu duka shi kadai

Malam Mele ya ce suna ta fafutukar ganin yadda za su haɓaka yawan man da ake haƙowa domin ci gaban ƙasar da kuma saukakawa al’umma.

“An taɓa haƙo ganga miliyan biyu da dubu ɗari biyar a sehkarun baya, amma daga nan aka yi ta fama da rashin saka jari da kuma rashin tsaro har ta kai man da kae haƙo wa ya yi ƙasa zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a wannan shekara,” in ji shi.

Ya ce hakan ne ya sa suka tashi da yin aiki tukuru don samo bakin zaren matsalar.

“Amma zuwa watan Yuni mun ka zuwa ganga miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas,” in ji Kyari.

Karanta Wannan  SUBHANALLAH: An wayi gari da ambaliyar ruwa da ba'a taba ganin irinsa ba a cikin garin Maiduguri. Ruwa ya shafe gidajen mutane a halin da ake ciki yanzu haka

Ya ce nasarar za ta sa a samu ƙarin arziki a ƙasar da haraji da sauransu.

“A iya sanina babu dogayen layukan mai ba a Najeriya. Cire tallafi ne ya janyo aka samu sauki,” in ji shugaban na NNPCL.

A ɗaya gefen, Malam Lawal Musa babban mai ba da shawara kan kasuwancin NNPCL, ya ce an samu ƙaruwar yawan gas ɗin da ake haƙowa a kasar.

NNPCL ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, ya cire haramtattun bututan layin mai daga jikin nasa da ya kai 5,800.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *