
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, sun yi kokari sai wajan nasarar kubutar da daliban makarantar MAGA na jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa, yana jinjinawa jami’an tsaro kan namijin kokarin da suka yi wajan wannan nasara da aka samu.
Yace sun gudanar da aikinne bisa umarnin shugaban kasa Bola Tinubu.