Tuesday, May 19
Shadow

Kai Duniya: Ji yanda Wani Marar Imani ya tsallaka Maqabara ya Qàqùlò Qàbàrìn Jariri a Potiskum, Jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yobe na cewa, wani mutum ya tsallaka katangar maqabartar Potiskum ya tone Qabarin wani jariri sannan ya tsere da gawar.

Kakakin ‘yansandan jihar,  SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya koka da yawaitar tone-tonen Qaburbura a jihar.

Inda yace ko a farkon watannan sai da suka samu Rahoton irin hakan a Karamar hukumar Jakusko inda har yanzu suna neman wanda ake zargin.

Kwamishinan ‘yansandan jihar CP Emmanuel Ado ya yi Allah wadai da lamarin inda ya baiwa duk DPO dake fadin jihar umarnin su saka ido a maqabartun jihar dan hana irin haka faruwa.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Kaptin din Najeriya, Wilfred Ndidi yace kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles su ci gaba da Atisaye kawai, Idan Gwamnati bata biyasu hakkinsu ba shi zai biya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *