
Dattawan Yarbawa mazauna babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
A sanarwar da suka fitar sun ce Tinubu ya cancanci ya sake tsayawa takarar shugaban kasa.
Sun ce kuma ‘yan Adawa masu son kayar dashi zabe su sani shi zabin Allah ne.