Gwamnatin Tarayya ta yiwa ‘yan Najeriya godiya bisa hakurin da suke yi da matsin rayuwa da suka shiga saboda tsare-tsaren gwamnatin.
Hakan ya fito ne daga bakin ministan kudi, Wale Edun inda yake ganawa da ‘yan majalisar tarayya.
Yace ‘yan Najeriya sun cancanci yabo bisa hakuri da juriya da suka nuna inda gashi yanzu har an kawo matakin moriyar wadannan gyare-gyaren.
Ministan yace manya-manyan gyare-gyaren da suka yi sune cire tallafin man fetur da cire tallafin dala wanda kuma yanzu an fara ganin nasarar wannan mataki nasu.