Monday, December 9
Shadow

Muna matukar godiya da hakuri da kuke yi da wahalar da tsare-tsaren gwamnatin mu suka jefa ku ciki amma yanzu lamura sun fara Gyaruwa>>Gwamnatin Tarayya ga ‘yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta yiwa ‘yan Najeriya godiya bisa hakurin da suke yi da matsin rayuwa da suka shiga saboda tsare-tsaren gwamnatin.

Hakan ya fito ne daga bakin ministan kudi, Wale Edun inda yake ganawa da ‘yan majalisar tarayya.

Yace ‘yan Najeriya sun cancanci yabo bisa hakuri da juriya da suka nuna inda gashi yanzu har an kawo matakin moriyar wadannan gyare-gyaren.

Ministan yace manya-manyan gyare-gyaren da suka yi sune cire tallafin man fetur da cire tallafin dala wanda kuma yanzu an fara ganin nasarar wannan mataki nasu.

Karanta Wannan  Kalli Hoto: Tsohuwar 'yar kwallon Najeriya da Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad ya dauki nauyinta zuwa kasar Amurka aka mata aiki ta koma Namiji na neman taimakon Naira Miliyan 69.7 dan a mata karin aikin da zata rika haihuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *