Thursday, September 24
Shadow

Shugaban ‘Yansandan Najeriya ya bayar da umarni ga ‘yansanda su daura bakin kyalle dan nuna Alhinin rayuwar shugaban sojoji

Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Kayode ya bayar da umarni ga ‘yansandan kasarnan da su daura bakin kyalle na tsawon kwanaki 7 dan nuna alhinin rasuwar shugaban sojoji Lt. Gen. Taoreed Lagbaja.

Kakakin ‘yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Yace wannan matakine da aka dauka dan girmama tsohon shugaban sojojin da kokarin da ya nuna wajan yaki da matsalar tsaro.

Karanta Wannan  A karo na biyu, Yaron dan Damisa ya dake fitar da Bidiyon inda yace yaga ana yada Bidiyonsa wai yana bàràzànà kan wanda ke murna da rashin me gidansu to tabbas hakane ya gargadi masu murnar su shiga taitayinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *