Sunday, December 14
Shadow

Munafurci da rashin aikin yi ne ke damunka>>Shehu Sani ya Gayawa El-Rufai kan caccakar Gwamnatin Tinubu

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya soki tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda sukar Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

A martanin da yawa El-Rufai ta shafin X, Shehu Sani yace rashin aikin yi da kuma damuwa da munafurcine suka dabaibaye El-Rufai.

Yace a lokacin yana gwamnan Karaduna, El-Rufai bai dauki ‘yan adawa a matsayin komai ba, amma wai yau shine yake nuna yana tare da ‘yan adawa.

Yace kawai dan ba’a bashi mukami a Gwamnatin Tinubu bane abin ke damunshi yake ta bi yana bata Gwamnatin.

A baya dai, El-Rufai ya bayyana cewa jahilaine a cikin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

Shehu Sani ya kara da cewa a yanzu El-Rufai yana ta bine duk wani taron dattawa a Arewa yana yada manufar bangaranci da raba kai.

Karanta Wannan  Duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam'iyyar APC ba, masu koma kuwa suna yi ne dan samun na Abinci>>Tambuwal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *