Friday, February 7
Shadow

Magidanci ya kkashe diyarsa me shekaru 15 saboda yin TikTok

Wani magidanci a kasar Pakistan ya kashe diyarsa saboda ta na yin Bidiyon TikTok wanda baya so.

Mutumin me suna Anwar ul-Haq bai dade da komawa kasarsa ta Pakistan ba daga kasar Amurka tare da diyarsa wadda ya haifa a can.

Rahotanni daga kafar yada labarai ta kasar Pakistan Geo News sun ce Anwar ya harbe diyar tasa ne a kan titi a Balochistan’s Quetta ranar Talata.

Jami’in dansanda, Zohaib Mohsin yace an kama Anwar inda da farko yayi ikirarin cewa wani dan Bindiga ne da ba’a san kowanene ba ya kashe diyar tasa amma daga baya ya amsa cewa shine.

A kasar Pakistan dan dangi kan kashe mata idan suka jawo musu abin kunya.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Shugaba Tinubu ya gana da yariman Saudiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *