
Malami me da’awa a kafafen sada zumunta, Dr. Hussain Kano ya bayyana cewa, Munin Laifin wanda suka je Maulidi a Katsina yafi na wanda suka yiwa matar aure da ‘ya’yanta aika-aika a Dorayi Kano.
A cewarsa, masu Maulidi shirka suka aikata su kuma wancan na Kano, Laifi ne suka aikata wanda idan Allah ya ga dama zai iya yafe musu.
Wannan kalamai nasa dai sun jawo cece-kuce sosai.