Saturday, December 21
Shadow

Mutane 243,000 sun daina biyan kudin talabijin ta DSTV a Najeriya saboda tsadar rayuwa

Rahotanni sun nuna cewa mutane 243,000 sun daina biyan kudin DSTV da GoTV saboda tsada rayuwa.

Kamfanin wanda na kasar Afrika ta kudu ne ya bayyana cewa ya rasa wadannan mutanen ne daga watan Afrilu na wannan shekare zuwa watan Satumba na shekarar.

An ga hakanne a cikin bayanan yanda kamfanin ya gudanar da kasuwancinsa wanda ya fitar a karshen watan Satumba.

Kamfanin ya alakanta hakan da tsadar rayuwa wadda ta hana da tsadar kayan abinci, wutar lantarki, da man fetur.

Kamfanin ya kara da cewa, ya rasa mitane 566,000 a gaba dayan nahiyar Afrika wanda suka daina biyan kudin DSTV da GoTV din.

Karanta Wannan  Gwamnan Zamfara ya ɗauki nauyin karatun zaƙaƙuran ɗaliban jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *