Saturday, April 26
Shadow

Na karbi mulki Najeriya na cikin wahala da matsin tattalin arziki shiyasa na dage dan kawo gyara>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya karbi mulkin Najeriya a yayin da take cikin wahalar rashin tabbas na tattalin arziki.

Shugaban yace shiyasa ya dauki matakai tsaurara musamman a bangaren kudi dan ganin ya kawo ci gaba.

Shugaban ya bayyana hakane a wajan rantsar da zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo inda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilceshi.

Yace a yanzu saboda matakan da ya dauka, kasar ta dauki hanyar ci gaba da nasara.

Karanta Wannan  Kasar Nijar ta koro 'yan Najeriya 148 da suka shigar mata kasa ba bisa ka'ida ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *