
Fasto Wale Oke na cocin Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN ya bayyana cewa matsalolin Najeriya sun fi karfin mutum ya gyarasu.
Yace dan hakane ma su ka yanke hukuncin ci gaba da yiwa Najeriya addu’a inda yace zasu ci gaba da azumi da addu’a kan Allah ya gyara Najeriya.
Yace kuma ya gayawa mutanensu cewa su shiga siyasa kada su yi baya-baya, su shiga a dama dasu. Ba wai maganar karbar katin zabeba, su tsaya takara suma a zabesu.