
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin tarayya inda yace basu dauki matakan da ya kamata ba gashi mutane na ta mutuwa.
Ya bayyana hakane a sakon ta’aziyya ga iyalan ‘yan kwallon Kano 22 da suka rasu a hadarin Mota. Inda yace ba iyalansu kadaine suka yi asararsu ba, hadda ma Najeriya baki daya.
Ya kuma bayyana Alhinin rasuwar mutane sama da 100 a ambaliyar ruwan garin Mokwa dake jihar Naira inda yace abin takaici ne.
Atiku ya baiwa Gwamnatin tarayya shawarar ta dauki matakan kula da titinan Najeriya dan rage ko kawar da yawaitr hadurra.
Sannan ya nemi da a dauki matakan hana ambaliyar ruwa musamman yanzu da ake fuskantar yawaitar ruwan sama.