
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya tarar da ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Borno dake zuwa aiki da wuri da sassafe a wata ziyarar ba zata.
Rahoton yace ya baiwa kowanne daga cikin ma’aikatan da ya tarar sun je aiki da wuri kyautar Naira Miliyan 2.
Da yawa sun yabawa gwamnan game da hakan da yayi.