Sunday, December 14
Shadow

Muzanta Naira: Kotu ta yanke wa wani dan Tiktok hukunci a Kaduna

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC reshen Kaduna ta samu nasara bayan da kotu ta yanke hukunci ga wani a mai amfani da shafukan Tiktok da Instagram, Muhammad Kabir.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban Mai Shari’a R.M. Aikawa na Babban Kotun Tarayya dake zamanta a Kaduna, bisa laifin wulakanta kudin Naira.

Shugaban sashen hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, jihar Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na Tiktok da Instagram (@youngcee0066), yana watsar da takardun kudi na Naira a ƙasa, yana taka su da kafa, tare da furta wasu kalmomi cikin harshen Hausa yana kalubalantar EFCC da ta zo ta kama shi a inda aka san yana zaune.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kasar Burkina Faso taqi sàkò sojojin Najeriya 11 data kama, Tàcè bata yadda kuskurene yasa suka shiga sararin samaniyarta ba da izini ba

An kama shi bisa karya dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) wadda ta haramta wulakanta wa da lalata takardun kudi.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Aikawa, ya yanke wa Muhammad hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira dubu dari uku (₦300,000.00) ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *