Sunday, March 29
Shadow

Na sadaukar da Albashina gaba daya tun daga farkon hawan mulkina a baiwa Iyalan sojojin da suka rigamu gidan gaskiya da kuma wanda suka jikata>>Inji Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya sadaukar da Albashinsa gaba daya tun daga hawansa mulki a 2023 zuwa ga iyalan sojoji da suka rigamu gidan gaskiya da kuma wadanda suka jikkata.

Shugaba Tinubu yace an bude wani asusu ne na musamman dan tallafawa irin wadannan sojoji da iyalansu, kuma shine shi ya fara saka tasa Gudummawar.

Yace yana kira ga Gwamnoni, Sanatoci da sauran ‘yan kasuwa da abokan sa suma su saka nasu gudummawar.

Ya bayyana cewa aikin na sojoji sadaukarwa ce wadda bai kamata a barta haka ba.

Karanta Wannan  Ƴansanda a Kano sun kama mutane 9 bayan rykycyn

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *