
Bishop David Oyedepo wanda ya kirkiri Cocin Living Faith ya bayyana cewa, Najeriya ba zata taba zama kasar Musulmai ba.
Ya bayyana hakane a cocin nasa yayin da yakewa mabiyansa jawabi.
Yace Cocin Najeriya ba za’a iya lalata ta ba.
Sannan masu kawo hari ‘yan Jìhàdìn Islama na yi suna yi.
Yayi Allah wadai da hare-haren da masu daukar nauyinsu inda yace gaba daya ya tsine musu Albarka.
Yayi kira ga mabiyansa da su dukufa da addu’a ta tsawon kwanaki 7 dan kawo karshen lamarin