
Rahotanni sun bayyana cewa, Naira Biliyan 128 ta bace a ma’aikatar wutar Lantarki ta Najeriya.
Kungiyar dake saka ido kan yanda ake kashe kudin Gwamnati, SERAP ce ta bayyana hakan
Ta bukaci a yi bincike dan gano inda kudaden suka shiga.
Saidai Ministan Wutar Lantarkin a martaninsa game da haka yace an sace kudin ne kamin ya zama ministan wuta domin bayanan da ake magana akansu na shekarar 2022 ne.