Friday, December 5
Shadow

Najeriya na fuskantar haɗarin faɗawa mulkin kama-karya – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce hare-haren da aka kai kan masu gudanar da taro a jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi a matsayin abubuwan da ke da haɗarin “jefa Najeriya cikin tsarin kama-karya a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.”

A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari tare da tayar da tarzoma a wani wurin taron ƴaƴan jam’iyyar hadaka ta ADC a birnin Kaduna.

Cikin mahalarta taron har da jiga-jigan jam’iyyar ta ADC, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma shugaban jam’iyyar na Arewa maso yamma.

Daga baya, a jiya Alhamis rundunar ƴansandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta aika da takardar gayyata ga jam’iyyar ta ADC da kuma jagororinta da su bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan hatsaniyar da aka samu a lokacin taron.

Karanta Wannan  Yadda Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umarah Ya Gaisa Da Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima A Fadar Shugaban Kasa, Yau Laraba

A cikin wata sanarwa da tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriyar ya fitar a shafinsa na X, Atiku ya ce “gayyatar da aka yi wa Nasir El-Rufai da harin da aka kai kan tawagar tsohon ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami da kuma tarwatsa taro kan matsalar tsaro na ƙungiyar dattijan Katsina” a matsayin abin damuwa.

“Wannan alama ce ta ƙokarin danne muryoyin al’umma da take hakkin fararen hula a tsari na dimokuradiyya”.

Siyasar Najeriya ta fara ɗaukar zafi ne tun kafin cika shekaru biyu na mulkin shugaban Najeriya, Bola Tinubu, bayan da wasu manyan ƴan adawar siyasa na ƙasar suka nuna aniyar hadewa wuri ɗaya domin ƙalubalantar shugaban ƙasar a babban zaɓen da za a yi a shekara ta 2027.

Karanta Wannan  Matar Rarara, A'ishatulhumaira ta aikawa Baana sammace inda tace ya mata Qazafin yin mu'amala da maza ciki hadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Wannan ne ya sanya manyan jagororin adawa kamar Atiku Abubakar, da Peter Obi da Nasir El-Rufai suka shiga jam’iyyar ADC, wadda suka ce za su yi amfani da ita a matsayin lemar ƙalubalantar shugaban mai ci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *