Wednesday, May 7
Shadow

Najeriya ta mayar da ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba

Hukumar shige da fice ta Najeriya ta tabbatar da mayar da wasu ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin wata sanarwar da babban kwanturolan hukumar mai lura da kan iyakar Illela – inda ta nan ne aka fitar da mutanen – Tony Akuneme ce mutanan sun haɗa da maza 51 da kuma mata 11, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar, NAN ya ruwaito.

Mista Akuneme ya ce jami’an hukumar ne suka yi wa mutanen rakiya daga shalkwatar hukumar shige da fice ta ƙasa da ke Abuja zuwa kan iyakar Illela da ke jihar Sokoto, cikin motocin bas biyu.

Karanta Wannan  Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta

Ya ƙara da cewa bayan tanatance takardunsu, an miƙa su ga jami’an ƴansandan Nijar da ke Birnin Konni.

A baya-bayan nan Najeriya mayar da ƴan ciranin da ke shiga ƙasar daga maƙwabtan ƙasashe ba tare da cikakkun takardun izini ba.

A watannin da suka gabata ma ƙasar ta mayar da wasu gomman ƴan ƙasashen Mali da Togo da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *