Gwamnatin tarayya tace nan da shekarar 2027 zata samar da wutar Lantarki ta awanni 20 kullun.
Saidai tace sharadin hakan shine sai ta samu maau zuba jari a bangaren Fetur da iskar gas wanda a yanzu babu su sosai.
Me baiwa shugaban kasa shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana haka a wata ziyara da ta kai kasar Africa ta kudu.
Tace za’a mayar da hankali ne wajan samarwa Birane da masana’antu karfin wutar lantarkin.