Wednesday, January 15
Shadow

Nasiha akan rayuwa

Rayuwa cike take da gwagwarmaya, wata rana ayi dariya, watarana a yi kuka.

Duk yanda za’a juya,ka yi kokari, sannan a yi addu’ar Allah kada ya raba mutum da imaninsa.

Kowa na da matsala, ta wani tafi ta wani, kada ka ga mutum cikin manyan kaya da babbar mota ka yi tunanin yana cikin jin dadi, da zai bude maka cikinsa,kai da kake tafiya a kasa watakila ka fishi nutsuwa.

Kada ka yawaita bayyana matsalarka a wajan jama’a, ya zamana cewa amininka ne kadai zaka baiwa labarin abinda ke faruwa da kai.

Idan ka ji gaba daya duniyar ta canja, ka kasa gane kanka, komai ka gwada yaki yi, ka koma ga Allah,ka yi ta zikiri, ka rika karatun Qur’ani.

Karanta Wannan  Maganin ciwon ido kowane iri

Ka koma ka nutsu ka duba kanka da yanayin da kake ciki, insha Allahu zaka samu mafita.

Ka koyi girmama mutane, saidai kada ka wulakanta kanka.

Kada ka zama kullun saidai a baka, kai ma ka rika kokarin bayarwa.

Ka rike sana’a daya me kyau wadda za’a sanka da ita,amma kada ka tsaya a kanta ita kadai,ko da a boyene, ka zuba jari a wani bangare da ba zai dauke maka hankali daga kan babbar sana’ar ka ba. Dalili kuwa shine, karamin misali,ka kalli Dangote yana gishiri, yana taliya, yana fulawa, yana sukari, yana siminti,yana magi, da sauransu.

Dalilin yin sana’o’i da yawa shine idan ka fadi acan,zaka tashi a can.

Ka yi kokarin zama da mutane lafiya, kada ka yadda ka zama kai kadaine me kudi a cikin danginku ko abokanka, ka yi abuta da kalarka, kada ka yi abuta da wanda baka son zama irinsu.

Karanta Wannan  Maganin sanyi kowane iri

Ka yi abuta da mutanen da zaku rika karuwa da juna, watau suna taimaka maka kaima kana taimaka musu.

Kada ya zamana kai kadai kake yin taimakon, ko kuma kai kadai ake taimakawa.

Idan mutum yace bai sonka, to ka kiyayeshi, kar ka yi gaba dashi amma ka yi nesa-nesa dashi a yi gaisuwa irin ta musulunci.

Ka yanke hulda ta kut da kut da duk wanda baya girmama ra’ayinka.

Ka so me sonka.

Ka gayawa wanda kake so irin yanda kake ji a zuciyarka. Saboda wataran ba zaka samu wannan damar ba.

Ka yi kokarin farantawa kanka kamin ka farantawa wani, ka so kanka fiye da kowa, ka fara biyawa kanka bukata kamin ka biyawa wani. Ka dauki kanka da muhimmanci sosai.

Karanta Wannan  Amfanin hakuri a rayuwa

Kada ka ajiye tsabar kudi da tunanin zaka yi arziki, gara ka sayi kadara ka ajiye.

Ka girmama ra’ayin mutane ko da ya banbanta da naka, amma ba dolene ka yadda dasu ba.

Ka girmama iyayenka dana wasu.

Kada ka gaji da zikiri.

Kada ka gaji da neman kudi.

Kada ka gaji da neman farin ciki da nutsuwa.

Kowane zamani nakane indai ya sameka da hankalinka da lafiyarka da Karfinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *