Monday, December 16
Shadow

NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na naira biliyan 2.1 a Legas da Fatakwal

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce jami’anta sun samu nasarar kama muggan ƙwayoyin da kuɗinsu ya kai kimanin naira biliyan 2.1 a biranen Legas da Fatakwal

Cikin sanarwar nasarar mako-mako da hukumar ke fitarwa ta ce a ranar Juma’a 31 ga watan Mayu, jami’anta tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas suka kama wasu manyan jakankuna maƙare ƙulli 320 na tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 164.50 da aka yi safararta daga Canada.

Hukumar ta ce ta kama mutumin da take zargi da safarar tabar – da aka yi ƙiyasin kuɗinta ya kai naira miliyan 960, – mai suna an kama Ughenu Nnaife Francis, wanda ya shaida wa jami’an hukumar cewa naira miliyan shida aka biya shi domin shigar da kayan Najeriya.

Karanta Wannan  Kalli Hoton matar da aka kama da harsasai 2000 zata kaiwa 'yan Bindiga a jihar Zamfara, da kuma wasu 'yan Boko Haram da suka tuba

NDLEA ta kuma ce a ranar 27 ga watan Mayu jami’anta da ke birnin Fatakwal suka wata kontena da aka shigar da ita ƙasar daga Indiya, inda jami’anta tare da haɗin gwiwar jami’an kwastam suka tare da tare da gudanar da bincike.

A lokacin binciken ne aka gano katan 1,750 na kwalaben kodin da nauyinsu ya kai kilogiram 26,250, inda a ciki aka samu kwalabe 175,000 da hukumar ta ce kuɗinsu ya kai naira biliyan 1,225,000,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *