
Sanata Aliyu Wamako ya bayyana cewa, baya goyon bayan janye jami’an ‘yansanda daga baiwa manyan mutane kariya.
Ya bayyana hakane a zaman zauren majaliaar Dattijai.
Sanata Wamako yace dalili kuwa shine masu garkuwa da mutane hankalinsu zai koma kan manyan mutanen su fara sacesu.
Ya bayyana cewa ya kamata a tashi tsaye a yaki masu sata da kashe mutanen ne ba a rika binsu da lalama ba.