Thursday, January 2
Shadow

Ni da ‘yan Najeriya muna cikin farin cikin gyara matatar mai ta Warri – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce “shi da ‘yan ƙasar suna cike da farin ciki” sakamakon gyara matatar mai ta garin Warri da kamfanin mai na NNPCL ya yi.

Wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na X ya ce “hakan zai ƙara wa ‘yan Najeriya ƙwarin gwiwa kan fatan da suke da shi game da alƙawuran da muka yi”.

Ya ƙara da cewa labarin “hanya ce mai kyau ta kammala shekarar 2024 idan aka ƙara da nasarar da aka samu kan matatar mai ta Fatakwal”.

Yayin wani taron manema labarai a yau Litinin, shugaabn kamfanin NNPCL Mele Kyari ya bayar da sanarwar cewa sun gyara matatar kuma ta ci gaba da aiki a matakin kashi 60 cikin 100 na ƙarfinta.

Karanta Wannan  Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya tsere ana saura kwanaki 2 ya mika mulki saboda tsoron kamun EFCC

A cewar Tinubu: “Tun da yanzu matatar Warri na aiki bisa kashi 60 cikin 100, tsarin gwamnatina na samar da tabbataccen makamashi yana kan hanya.

“Ina shawartar NNCPL ya hanzarta gyara matatar mai ta Kaduna da ɗaya matatar ta Fatakwal domin tabbatar da matsayin Najeriya wajen samar da makamashi a duniya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *