Friday, January 16
Shadow

Ni Musulma ce, Na taso Gidan mu Babana Musulmi ne amma mamana Kiristace kuma na rika zuwa Coci sannan ina sallah amma daga baya na zabi Musulinci>>Inji Sultana ta BBNaija

Tauraruwar BBNaija, Farida Sultana Auduson Ibrahim wadda aka fi sani da Sultana ta bayyana cewa ita musulmace.

Ta bayyana hakane a hirarta da Zita.

‘Yar shekara 25 data fito daga jihar Adamawa amma tana zaune a Abuja me tallar kayan sawa tace ta taso gidansu Mahaifinta musulmi mahaifiyarta Kirista.

Tace mahaifinta dan jihar Adamawa ne musulmi kuma mahaifiyarta ‘yar jihar Cross River ce kirista, tace ta rika zuwa coci da masallaci a lokacin tana karamar yarinya sannan har an mata wankan tsarki na Kiristanci wanda tace kuma an bata sunan Josephine.

Sultana tace amma daga karshe ta zabi Musulunci saboda ta ga shine yafi dacewa da ita.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo inda Sheikh Dr. Musa Salihu Alburham yake cewa, Digital Imam yanda ya mayar da Wiy wiy kamar shayi, sannan ya yiwa 'yan mata da dama.... Bidiyon ne dai yasa 'ya'yan Digital Imam Mayar da Raddi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *