
Tauraron me wasan Barkwanci, Ayatullahi Tage ya bayyana cewa, shine ya fara saka mawaki Hamisu Breaker a kafafen sada zumunta a matsayin mawaki.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Gabon Show.
Ayatullahi Tage yace shine ke kula da YouTube din Hamisu Breaker amma daga baya aka rika zarginsa akai.
Yace ya nemi Hamisu Breaker ya bashi dubu 30 ya mikamai YouTube channel din amma abu ya faskara.
Yace daga karshe dai ya mikawa Hamisu Breaker shafinsa inda har yanzu gara lokacin yana hannunsa yafi tafiya yanda ya kamata.
Tage dai yace a yanzu ya koyi rayuwa shi kadai.