Monday, April 6
Shadow

NNPP tace ba zata baiwa Kwankwaso takara a 2027 ba

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa, ba zata baiwa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso takara a zaben shekarar 2027 ba.

Jam’iyyar ta bayyana hakane ta bakin sakataren ta, Mr. Ogini Olaposi a sanarwar da ya fitar ranar 12 ga watan Janairu.

Ya bayyana cewa jam’iyyar zata baiwa asalin ‘yan jam’iyyar masu kishinta takara ne.

Hakan na zuwane biyo bayan rashin jituwar da aka samu tsakanin Kwankwaso da jam’iyyar ta NNPP.

Karanta Wannan  A karshe Dai: Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kama jarumin Tik-Tok Ashiru Idris Mai Wushirya bisa tuhume tuhumen yin bidiyøñ da suka sabawa addini da al’ada a kafar Tiktok.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *