Wednesday, January 8
Shadow
Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Za a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi ya zama dole wajen gyara tattalin arzikin kasar, duk kuwa da kara wahalhalun da ake fuskanta da ke janyo fushin jama'a. Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na jiya a yayin bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya. “Na fahimci matsalolin tattalin arziki da muke fuskanta a matsayinmu na kasa. Tattalin arzikinmu yana cikin tsananin bukatar gyara shekaru da yawa. Ba a daidaita shi ba saboda an gina shi a kan kura-kurai na dogaro da kudaden shigar da ake samu daga hako man fetur,” inji Tinubu. Tun bayan hawansa ƙaragar mulki a bara, Tinubu ya cire da tallafin man fetur wanda ya haddasa tashin gwauron zabin sufuri da farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi a fadin kasar. Dubban ‘yan Najeriya ne suka fito kan t...
Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Ba mu cimma yarjejeniya da gwamnati kan mafi ƙarancin albashi ba – NLC

Siyasa
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma'aikata mafi karanci a ƙasar. Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000. A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago. Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi. Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeya...
Masu fama da kwalara na ƙaruwa a Najeriya

Masu fama da kwalara na ƙaruwa a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar da sanarwar fadakar da jama'a game da ƙaruwar kamuwa da cutar kwalara a fadin kasar yayin da damina ke ƙara kamari. An samu rahoton bullar cutar a jihar Legas a baya-bayan nan, lamarin da ya ƙara dagula al'amura. Daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Yunin 2024, an samu jimillar mutum 1,141 da ake zargi da kamuwa da cutar kwalara da kuma 65 da aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma mutum 30 sun ne suka mutu duk daga ƙananan hukumomi 96 a faɗin jihohi 30 sakamakon cutar. Jihohin da suka fi fama da cutar, waɗanda ke bayar da kashi 90% na yaɗuwar cutar sun hada da Bayelsa da Zamfara da Abia da Cross River da Bauchi da Delta da Katsina da Imo da Nasarawa da kuma Legas. Kungiyar kwararru kan hana yaɗuwar cuttutuka ta ka...
Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Siyasa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mayar da martani kan faduwar da ya yi lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2024. Bidiyon faduwar shugaban ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ya nuna Tinubu a lokacin da yake yunkurin shiga motar faretin a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda ya rasa wani mataki wajen hawar motar ya faɗi. Tinubu mai shekaru 72, ya ce dimokraɗiyya ta cancanci faduwa. Da yake magana game da abin da ya faru a ranar Laraba, shugaban ya yi dariya da cewa "na rusuna ne don girmama dimokraɗiyya" a salon Yarbawa. Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da taron liyafar cin abincin na bikin dimokraɗiyya wajen kira ga hadin kan Nijeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ko siyasa ba. Ya kuma jaddada cewa hadin kan Najeriya ba abu ne da za a iya yi...
Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Tsaro
Wasu ƴan bindiga sun kai wa wata tawagar sojoji da ke sintirin aikin sa ido kan bututun man fetur a garin Tibiri da ke yankin Dosso a kudu maso yammacin Nijar harin kwantan ɓauna inda suka kashe sojoji akalla shida. Rahoton wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta ya kara da cewa soja ɗaya ya ɓata sannan an lalata motoci biyu a harin. Rahoton bai bayyana ko an samu asarar rai a ɓangaren ƴan bindigar ba, ko kuma bayyana alakarsu da wasu ƙungiyoyi. Ƴan bindiga dai sun kasance suna gudanar da ayyukansu a wasu sassan Nijar da ke kan iyaka da arewa maso yammacin Najeriya. Har yanzu dai rundunar sojin ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba. Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, al'amuran tsaron ƙasar Nijar ke ƙara taɓarɓarewa, inda a lokuta da dama ...
Kotu na da hurumin sauraron ƙara kan masarautar Kano

Kotu na da hurumin sauraron ƙara kan masarautar Kano

Kano
Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan rikicin masarautar Kano, musamman kan abin da ya shafi kare hakkin ɗan'adam bisa dogaro da sashe na 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya. Alƙalin kotun, mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke jihar, ya yanke hukuncin cewa tsohon sarki Aminu Ado Bayero na da damar a saurare shi a kotu. Sai dai alkalin ya ce ba magana ce a kan cancantar majalisar dokokin jihar na sauya dokar masarautun jihar ko kuma a'a ba. Alƙalin ya bayyana cewa kotun ba ta ƙalubalantar damar da gwamnatin jihar ke da shi na naɗawa ko sauke sarki. A ranar 23 ga watan Mayu ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, bayan majalisa ta amince da ita. Wann...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin horas da ƴan awaren IPOB a Abia

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar dakarun Task Force Tactical Patrol Squad sun kai wani samame a wani sansanin horas da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da takwararta ta ESN a unguwar Ihechiowa na ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar Abia. A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kutsawa tare da tarwatsa sansanin da kuma lalata dukkan na’urorin horas da mayaƙan da kuma kayayyakin da aka samu a wurin. Rundunar sojin ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X. Cikin wata sanarwa da da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce samamen da sojojinta suka kai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin IPOB da ESN ke yi, waɗanda ke da alaka da kalubalen tsaro da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan ‘yan ƙasa da ...
Messi ba zai buga wa Argentina gasar Olympics ba

Messi ba zai buga wa Argentina gasar Olympics ba

Kwallon Kafa
Tauraron ɗan wasan Argentina Lionel Messi ya ce ba zai shiga cikin tawagar ƙasarsa ta 'yan ƙasa da shekara 23 ba yayin gasar wasanni ta Olympics. A madadin haka, Messi mai shekara 37 zai mayar da hankali kan buga gasar Copa America da za a fara a watan nan. "Na faɗa wa kociya Mascherano kuma gaskiya mun fahimci matsalar," kamar yadda Messi ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta ESPN. "Da wuya [mutum ya dinga tunanin Olympics yanzu] saboda Copa America ne a gabanmu. Zai zama wata biyu ko uku zan yi ba tare da ƙungiyar [Inter Miami] ba kenan, kuma yanzu shekaruna sun wuce a ce na shiga komai da komai. "Ya kamata na duba da kyau, abin zai yi yawa idan na buga gasa biyu a jere. Na yi sa'a sosai da na buga Olympics kuma na lashe gasar tare da Mascherano." Argentina da Messi za su ...
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Kaduna, Katsina
Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.. Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina. Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi. Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi...
Goron Sallah: Gwamnan Sokoto ya bai wa ma’aikatan jihar naira 30,000

Goron Sallah: Gwamnan Sokoto ya bai wa ma’aikatan jihar naira 30,000

Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da bai wa ma'aikatan jihar naira 30,000 a matsayin goron sallah. Cikin wata sanarwa da kwamishinan muhalli na jihar, Nura Shehu ya aike wa BBC, ta gwamnan jihar ya amince da bai wa duka ma'aikatan jihar da ƙananan hukumomi da masu fansho goron sallar. Sanarwar ta ƙara da cewa su ma ma'aikatan wucin gadi masu karbar alawus-alawus za su amfana da goron sallar. ''Rukuni na farko ya haɗa da ma'aikatan Jiha, da na ƙananan hukumomi za su karɓi naira 30,000 a matsayin goron Sallah'', in ji sanarwar. Sanarwar ta kuma ce ''rukuni na biyu da ya ƙunshi masu karɓar fansho da masu karɓar alawus-alawus a ƙananan hukumomi da kuma masu karɓar alawus-alawus a hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko waɗanda za su karɓi naira 20, 000 a matsa...