A shekarar 2023, na shirya mulkin Najeriya yanda ya kamata amma Tinubu bai shirya ba>>Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a shekarar 2023 ya bayyana cewa, ya shirya mulkin Najeriya amma Shugaban kasaz Bola Ahmad Tinubu bai shirya ba.
Saidai Atiku yace amma Tinubu bai makara ba, zai iya daukar matakan da suka kamata wajan magance matsalolin kasarnan idan da gaske yake.
Atiku ya bayyana hakane a sakon da ya fitar na cikar mulkin Bola Ahmad Tinubu shekara daya akan mulki.
Ya kara da cewa, Tinubu da mukarrabansa basu san hanyar da zasu dauka ba wajan magance matsalolin Najeriya, suna canki cankane akan abinda suke tunanin zai iya yin aiki.