Wacce jahace asalin hausa
Jihar Katsina itace tushen Hausa.
Garin Daura dake jihar Katsina shine tushen Hausa.
Anan ne aka samu labarin bayajidda.
Saidai duk da haka wasu masana musamman na zamani suna karyata cewa Akwai labarin bayajidda.
Hakanan wasu na tantamar cewa Daura ce tushen Hausa.
Akwai masu ganin cewa, Jihar Kano itace tushen Hausa.
Sannan akwai masu ganin cewa jihohin Kebbi, Zamfara da Sokoto ne Tushen Hausa.
Abin tabbatarwa kawai shine, Jihohin Arewa maso yamma sune Asalin Hausa wanda anan ne Hausawa suka fi yawa.
Akwai Hausawa a kasashen Nijar, Kamaru, Chadi, Central Africa Republic da sauran wasu kasashen da ba za'a rasa ba.