Wednesday, December 17
Shadow
An kai karin jami’an tsaro dubu 10 Jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

An kai karin jami’an tsaro dubu 10 Jihar Rivers bayan dakatar da Gwamna Fubara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Rivers na cewa,karin jami'an tsaron Civil Defense dubu 10 ne aka kai jihar Rivers dan su samar da tsaro bayan dakatar da Gwamna Fubara. Rahotannin sun ce an kai jami'an tsaronne dan su hadu da sojoji da sauran jami'an tsaron dake jihar dan su samar da tsaro ga bututun man fetur dake jihar. Kakakin hukumar ta Civil Defense, Afolabi Babawale ya tannatar da hakan, yayi kira da a daina fasa bututun man inda yace jami'ansu dubu 10 ne aka kai jihar ta Rivers dan su hana hakan. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya dakatar da Gwamna Fubara bayan da aka fasa bututun man fetur a jihar har sau 3.
Doka bata baka damar tsige zababben Gwamna ba>>El-Rufai ya gayawa Tinubu

Doka bata baka damar tsige zababben Gwamna ba>>El-Rufai ya gayawa Tinubu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon Gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa, doka bata bashi ikon tsige zababben gwamna ba. El-Rufai ya bayyana hakane jawabin da ya wallafa a shafinsa na X. Yace tabbas shugaban kasa na da cikakken iko amma ikonsa bai hada da tsige zababben gwamna ba. Ya bayyana cewa, dakatar da gwamnan jihar Rivers da Tinubu yayi ba daidai bane inda yayi kiran a mayar da Simi Fubara kan mukaminsa. Yace tabbas dalilin da shugab...
Kalli Bidiyo: El-Rufai yana yawan taimakon mutane amma daga baya sai su ci amanarsa>>Inji Gwamnan Kaduna, Malam Uba sani

Kalli Bidiyo: El-Rufai yana yawan taimakon mutane amma daga baya sai su ci amanarsa>>Inji Gwamnan Kaduna, Malam Uba sani

Duk Labarai
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na da yawan taimako amma matsalar da ake samu shine mafi yawan lokuta mutane na yaudararsa ne ko suna cin amanarsa. Ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. Yace Tunda yake da El-Rufai bai taba ganin yana kokarin siyasa kansa gida ba ko iyalansa, a ko da yaushe yana kokarin taimakon mutanene. Yace dan haka suna tare dashi kuma zasu bashi kariya da goyon baya. Kalli Bidiyon anan Da alama dai wannan tsohon Bidiyone dan kuwa tuni dangantaka ta yi tsami tsakanin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Gwamna Uba Sani inda El-Rufai ya fada a gidan talabijin na Arise TV cewa Uba Sani ba abokinsa bane, sun bata.
Kalli Bidiyo DA ƊUMI-ƊUMI: An Samu Fashewar Tankar Man Fetur A Yammacin Wannan Rana Ta Laraba A Dai-dai Kasan Gadar Karu Abuja Kan Hanyar Zuwa Keffi A Kalla Sama Da Motoci 20 Ne Suka Ķone

Kalli Bidiyo DA ƊUMI-ƊUMI: An Samu Fashewar Tankar Man Fetur A Yammacin Wannan Rana Ta Laraba A Dai-dai Kasan Gadar Karu Abuja Kan Hanyar Zuwa Keffi A Kalla Sama Da Motoci 20 Ne Suka Ķone

Duk Labarai
An Samu Fashewar Tankar Man Fetur A Yammacin Wannan Rana Ta Laraba A Dai-dai Kasan Gadar Karu Abuja Kan Hanyar Zuwa Keffi A Kalla Sama Da Motoci 20 Ne Suka Ķone. Idan Kana Da Mutanen Dake Bin Hanyar Karu, Nyanya Maraba A Abuja, Ko Zama Wadannan Yankuna, To Ku Kira Su Ku Ji Don Sanin Ko Suna Cikin Koshin Lafiya, Saboda Tankar Mai Ta Fashe A Hanyar Abuja Zuwa Nyanya, Inda Ta Yi Sanadiyar Mùțùwar Mutane Da Dama A Daidai Lokacin Shan Ruwa A Yau Laraba Jama'a a taimaka a yada (sharing) domin sako ya isa ga jama'a. Daga Yãhäyæ Yàküßù Àlhãssāñ. Kalli Bidiyon anan Kalli Karin Bidiyo Kalli karin Bidiyo anan
Ku Daina Takalarmu, Tinubu zai iya tsige kowane gwamna, na jihar Rivers ne tsautsai ya fada kanshi ya zama na farko>>Tinubu ya gargadi Gwamnoni

Ku Daina Takalarmu, Tinubu zai iya tsige kowane gwamna, na jihar Rivers ne tsautsai ya fada kanshi ya zama na farko>>Tinubu ya gargadi Gwamnoni

Duk Labarai
Babban lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi ya kare matakin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers. Inda yace shugaban kasar na da karfin ikon dakatar da kowanw Gwamna. Fagbemi ya gargadi gwamnonin cewa duk gwamnan dake neman zama barazana ga Gwamnatin Tinubu na iya fuskantar dakatarwa. Yace a yau gwamnan jihar Rivers ne a gobe zai iya zama kowane Gwamna. Ya gargadi cewa babu wanda zasu bari ya mayar da Dimokradiyya abin wasansa.
Bidiyo Da Duminsa: Mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti sun fara zaben dan yi mata kiranye ta sauka daga wakilcinsu da take a majalisar Dattijai

Bidiyo Da Duminsa: Mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti sun fara zaben dan yi mata kiranye ta sauka daga wakilcinsu da take a majalisar Dattijai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi sun fara yin zabe dan yi mata kiranye ta dawo daga wakiltarsu da take a majalisar Dattijai. Bidiyo ya nuna yanda tuni aka fara kada kuri'a dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye. Sanata Natasha Akpoti dai ta zargi kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da nemanta da lalata zargin da ya karyata. Dalilin haka aka dakatar da ita daga ayyukan majalisar na tsawon watanni 6. kalli Bidiyon zaben anan
Shugaba Tinubu ya rantsar da Gwamnan Rikon kwarya na jihar Rivers

Shugaba Tinubu ya rantsar da Gwamnan Rikon kwarya na jihar Rivers

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Étè Ibas (retd.). Bikin rantsarwar ya samu halartar shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila, da babban lauyan Gwamnati, Mr Lateef Fagbemi, SAN, da kuma sakataren shugaban kasa, Mr Hakeem Muri-Okunola. Da misalin karfe 12:48 pm ne Ibas ya shiga fadar Shugaban kasar.
Kamfanin mai na Dangote ya sanar da daina siyar da mai a Naira

Kamfanin mai na Dangote ya sanar da daina siyar da mai a Naira

Duk Labarai
Kamfanin matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetir da kuɗin Najeriya wato Naira. Kamfanin ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya aike wa dilallan man fetir a yau Laraba. Sanarwar ta ce ''Kamfanin tatar mai ta Dangote ta dakatar da sayar da fetir a naira na wani lokaci. Hakan ya zama wajibi ne saboda kaucewa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribarmu da kuɗin da muke sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala muke yi.'' Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne su sauya kuɗin da suke siyar da man domin ya yi dai-dai da kuɗin da su ke siyan ɗanyen mai na wani ɗan lokaci. Sanarwar ta kuma ce kamfanin ya dukufa wajen biyan buƙatun kasuwannin Najeriya, kuma da zarar sun karɓi jiragen dakon mai da aka siya da Naira d...
Gwamnatin tarayya zata sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar Rivers kudaden jihar ta aka rike

Gwamnatin tarayya zata sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar Rivers kudaden jihar ta aka rike

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kudaden jihar Rivers da aka rike zasu sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar karkashin kulawar Vice Admiral Ibok Ibas (retd). Gwamnatin tace matakin da shugaba Tinubu ya dauka a jihar Rivers ya daukeshi ne a daidai lokacin da ya dace dan kaucewa lalacewa al'amura a jihar. Gwamnatin ta kuma ce, Tsohon gwamnan jihar, Nyesome Wike bashi da hannu a wajan rikicin siyasar jihar da ya kai ga saka dokar tabacin. Babban akanta janat na kasa, Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Laraba. Ya bayyana cewa shin sai yaushene ake son ganin shugaba Tinubu ya dau wannan mataki? Yace sai abubuwa sun rinchabe? Yace yanzu ne daidai lokacin da ya kamata a dauki matakin.
Za mu bi hanyoyin da doka ta tanada wurin dawo mana da haƙƙinmu – Fubara

Za mu bi hanyoyin da doka ta tanada wurin dawo mana da haƙƙinmu – Fubara

Duk Labarai
Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar Siminalayi Fubara ya ce tun hawansa mulki, ya yi ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma kawo cigaba a jihar, sai dai ƴan majalisar dokokin jihar suna ta kawo cikas ga ƙoƙarin nasa. Gwamnan da aka dakatar ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar bayan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da shi da mataimakiyarsa na watanni shida saboda rikicin siyarsa da ya ki ci ya ki cinyewa. Fubara ya ce dukkanin abubuwan da ya yi da matakan da ya ɗauka ya yi su ne bisa rantsuwar da ya sha na kama aiki, inda ya ce hakan ne ya sa bayan da shugaba Tinubu ya shiga tsakani, ya yi gaggawar aiwatar da yarjejeniyar da aka amince ciki har da dawo da kwamishinonin da suka ajiye aiki. Ya kuma ce ba su yi ƙasa a ...