Gwammatin Tinubu tace zata gina makamin kare dangi, watau Nokiliya, Saidai Minista yace kul kada a fara
Ministan wutar Lantarkin Najeriya, Adebayo Adelabu ya gargadi yunkurin hukumar makamashin Najeriya na samar da tashoshin makamin Nokiliya dan samar da wutar lantarki.
Hukumar dai tace tana son yin hakanne dan samar da wutar Lantarki me karfin 1,200 Megawatt da zata magance matsalat wutar Lantarkin Najeriya.
Shugaban Hukumar Makamashin, Anthony Ekedewa ya kaiwa ministan wutar lantarkin ziyara a ofishinsa a Abuja ranar Talata ind ya bayyana cewa suna shirin samar da tashoshin makamin kare dangi guda 4 a Najeriya.
Yace idan suka yi nasara hakan zai samar da ingantacciyar wutar Lantarki me karfi sosai a Najeriya
Yace suna son kafa wadannan tashoshin wutar ne a jihohin Kogi da Akwa-Ibom.
Saidai yace basu da kudi amma suna neman hada kai da ma'aikatar wutar Lantarkin.
Mini...








