Friday, May 15
Shadow

Ba zamu iya ci gaba da biyan tallafin wutar Lantarki ba>>Gwamnatin Tarayya

Shugaban kwamitin dake kula da yanda Gwamnatin tarayya ke kashe kudi, James Faleke ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ba zata iya ci gaba da biyan kudij tallafin wutar lantarki ba.

Ya bayyana hakane yayin da ma’aikatar kudi ke bayanin yanda zata kashe kudadenta a shekarar 2025.

Gwamnatin tarayya dai ta ware Naira biliyan 705 dan biyawa ‘yan Najeriya tallafin wutar a shekarar 2025.

Saidai Falake yace sam babu bukatar hakan musamman lura da yanda farashin wutar labtarkin ke ta kara tashi kullun da kuma yanda darajar Naira ke ci gaba da faduwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda Ministar Al'adu da Yawon Bude Ido, Hannatu Musa Musawa ta dauki wata tsohuwa dake tafiya da kyar zuwa masallaci a motarta, ta kaita masallacin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *