Tuesday, December 16
Shadow
Mutanen da suke juya gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Dalung

Mutanen da suke juya gwamnatin Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Dalung

Duk Labarai
Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya a zamanin shugaba Buhari, Solomon Dalung, ya ce mutanen da ke juya gwamnati ta bayan fage waɗanda ake kira 'cabal' na mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu sun fi na zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari haɗari. Dalung ya bayyana haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels a ranar Talata, inda ya ce a zamanin mulkin Buhari, wasu mutane sun riƙa juya akalar gwamnatin. Sai dai ya ce waɗanda suka juya mulkin Buhari ba su da ilimi da wayewa sosai, amma waɗanda suke juya gwamnatin Tinubu sun fi ilimi da sanin mulki kuma sun fi tarin buri. Dalung ya ce, "lallai akwai masu juya gwamnati ta bayan fage a zamanin Buhari. Amma mutanen wancan lokacin ba su da ƙwarewa sosai a kan mulki da siyasa, don haka tasirin ya taƙaitu. Amma...
EFCC ta tsare jami’anta 10 bisa zargin satar kayan aiki

EFCC ta tsare jami’anta 10 bisa zargin satar kayan aiki

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta tsare jami'anta 10 game da zargin hannunsu a ɓacewar wasu kayayyakin aiki. An kama jami'an ne a makon da ya gabata, kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukan zumunta ta bayyana yau Laraba. "Jami'an da aka kama makon da ya gabata bisa umarnin Shugaba Ola Olukoyede, na amsa tambayoyi game da ɓatan wasu kayayyakin aiki," in ji kakakin EFCC Dele Oyewale. Wannan sanarwa na zuwa ne bayan hukumar ta sanar da korar jami'an nata 27 a shekarar da ta gabata saboda "zambatar mutane" da sauran laifuka.
Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi kasa daga Kano zuwa Kaduna

Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi kasa daga Kano zuwa Kaduna

Duk Labarai
Bankin raya ƙasa na China ya bai wa Najeriya rancen dala miliyan 254.76 domin gina titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna. Sanarwar da bankin ya fitar na zuwa ne gabanin ziyarar ministan harkokin wajen China a Najeriya cikin mako mai zuwa. Minista Wang Yi zai isa Najeriya domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da sauran manyan jami'an gwamnatin tarayya tun daga ranar Laraba. Aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203, ana sa ran zai laƙume dala miliyan 973 amma ya dakata saboda ƙarancin kuɗi. "Idan aka kammala shi, layin dogon zai haɗe Kano, mai muhimmanci a arewacin Najeriya, da kuma Abuja babban birnin ƙasar, inda zai ba wa mutane damar yin tafiya mai sauƙi," a cewar sanarwar da bankin ya wallafa a shafinsa na intanet. Tun da farko gwamnatin Najeriya ta ce Exim Bank na...
Daga almajiranci na zama shugaban NNPC – Kyari

Daga almajiranci na zama shugaban NNPC – Kyari

Duk Labarai
Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce yana godiya ga Allah da ɗaga darajarsa daga wanda ya taɓa karatu a makarantar tsangaya ta amajirai har ya kai ga zama shugaban NNPCL a Najeriya. Mele Kyari ya bayyana haka ne a shafinsa na X, a saƙonsa na godiya ga Allah bisa cika shekara 60 a duniya. A cewarsa, "cikin ikon Allah, a yau nake cika shekara 60 a duniya, duk da na riga na kai tun a baya idan aka yi la'akari da watan musulunci. Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar zama shugaban kamfanin makamashi mafi girma a Afirka." Kyari ya ce yana godiya ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ma Najeriya bisa wannan damar da ya samu. "Idan na waiwayi baya, nakan tuna gwagwarmayar da na sha. Nasarori da ƙalubale waɗanda Allah ne kaɗ...
ICPC ta maka tsohon kwamishinan El-Rufai a kotu

ICPC ta maka tsohon kwamishinan El-Rufai a kotu

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa ta Najeriya ICPC ta maka kwamishina a tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Bashir Saidu a kotu bisa zargin almundahanar kuɗi. Jami'in shari'a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha ne ya gabatar da ƙarar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an maka Bashir Sa'idu a kotun ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa. A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a bara, ta zargi tsohuwar gwamnatin da almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.
Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kan sojojinta a jihar Borno. A wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce an kashe sojoji guda shida, sannan wani kwamandan ƴan sa-kai ya jikkata. Sai dai Buba ya ƙara da cewa a gumurzun, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan Boko Haram 34, sannan sun ƙwato wasu makamai. Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya. A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar da ke jihar Borno.
An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce an kusa fara biyan masu yi wa ƙasar hidima alawus na naira 77,000 da aka amince za a riƙa biyansu na wata-wata. Darakta-janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana haka a ranar Talata a wata sanarwa da kakakin NYSC, Caroline Embu ta fitar kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Ahmed ya ce zai mayar da hankali kan jin daɗin masu yi wa ƙasa hidima, inda ya ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun kammala domin fara biyan sabon alawus ɗin. An dai ƙara alawus ɗin ne tun bayan da gwamnatin Najeriya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar.
Ana barazanar kkasheni saboda na yi magana akan Peter Obi>>Inji Me magana da yawun APC, Felix Morka

Ana barazanar kkasheni saboda na yi magana akan Peter Obi>>Inji Me magana da yawun APC, Felix Morka

Duk Labarai
Me magana da yawun Jam'iyyar APC, Felix Morka ya bayyana cewa, an aika masa barazanar kisa har guda 400 wanda daga ciki guda 200 kai tsaye aka ce za'a kasheshi ko yankashi saboda yayi magana akan Peter Obi. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV inda yace an masa kazafin cewa ya yiwa rayuwar Peter Obi Barazana. Yace shi karya ake masa, babu inda yawa rayuwar Peter Obi Barazana. Yace tuni aka fara kaiwa wasu daga cikin 'yan uwansa hari inda yace ya dauki bayanai akan wannan barazana da ake masa inda zai kaiwa hukumar 'yansanda korafi. A baya dai, Shima Peter Obi yace ana yiwa rayuwarsa barazana.
Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Gidan Yari Na Jihar Katsina Ya Ziyarci Buhari Bayan Ya Karbi Ragamar Kama Aiki

Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Gidan Yari Na Jihar Katsina Ya Ziyarci Buhari Bayan Ya Karbi Ragamar Kama Aiki

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari, ya karɓi baƙuncin sabon shugaban ma'aikatan hukumar kula da gidan gyaran hali na jihar Katsina Mr. Umar Baba, a gidansa na Daura dake jihar Katsina Sabon Kwantirolan NIS Umar Baba, ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, a ranar 7 ga Janairu, 2025.
Farashin kayan Abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoman Arewa sun zabi kai kayan amfanin gonarsu kasashen waje

Farashin kayan Abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoman Arewa sun zabi kai kayan amfanin gonarsu kasashen waje

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa ana hasashen farashin kayan abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoma a Arewa sun zabin kai kayan abincinsu kasashen waje su sayar maimakon sayarwa a gida Najeriya. Manoma a jihohin Kaduna da Kwara sun koka da rashin amfanin gona me kyau saboda karancin ruwan sama da krkatar da kayan noman da 'yan siyasa suka yi. Saidai manoma a jihohin Jigawa, Kano da Yobe sun bayyana samun amfanin noma sosai irinsu Dawa, Wake, Masara, Gero da Sauransu. Saidai sun bayyana cewa, mafi yawancin kayan amfanin nasu zasu kaisu jihohin wajene dan sayarwa. Hakan a binciken jaridar Punchng ya nuna cewa, zai iya kaiwa ga hauhawar farashin kayan abinci a wannan shekarar.