Friday, December 19
Shadow
Hoto:Allura cikin ruwa, wannan zankadediyar budurwar ‘yar Najeriya dake zaune a kasar Amurka na neman Mijin aure, tace me ilimi take so wanda ya iya girki, dan tana aiki ita zata rike gidan, kuma dole ya iya tsaftace gida sannan dole ya zama gwarzo ne wajan kwanciyar aure

Hoto:Allura cikin ruwa, wannan zankadediyar budurwar ‘yar Najeriya dake zaune a kasar Amurka na neman Mijin aure, tace me ilimi take so wanda ya iya girki, dan tana aiki ita zata rike gidan, kuma dole ya iya tsaftace gida sannan dole ya zama gwarzo ne wajan kwanciyar aure

Soyayya
Wannan matashiyar me suna Ogechukwu Christine Kalu 'yar Najeriya ce dake zaune a kasar Amurka kuma ta bayyana cewa tana neman mijin aure. Matar dai ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta ranar 2 ga watan Yuli inda tace kalar mijin da take so shine me ilimi, wanda ya iya girki, ya iya gyaran gida kuma ya ita kwanciyar aure. Wannan magana tata ta dauki hankula sosai saidai wasu sunce mata da wuya ta samu kalar wannan namijin. "Now that my DM is clogged with “I love you” let me reinstate that I am single. Looking for a cute man, well educated, God fearing, knows how to pray and intercede for the family, can cook and enjoys laundry, is homely and can fold clothes immediately after laundry. Enjoys house chores, can take care of kids and also has a good job business and/or great c...

Hotunan mata 2 da suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran

Iran, Siyasa
Mata biyu ne suka fito takarar shugaban kasa a kasar Iran biyo bayan rasuwar tsohon shugaban kasar, Ebrahim Raisi a hadarin jirgin sama me saukar Angulu. Mace ta farko itace Zohre Elahian wadda 'yar majalisar tarayyar kasar ce kuma tana da karatu har zuwa digiri na 3 watau(Doctorate) a fannin physics. Sai kuma mace ta biyu me suna, Hamideh Zarabadi wadda itama 'yar majalisar tarayyar kasar ce kuma tana da digiri na 3 watau( Doctorate) a fannin engineering. Saidai kasancewar Iran kasar Musulmi ce da take riko da addinin musulunci sosai da kamar wuya su yadda su zabi mace a matsayin shugaban kasa.
Ji yanda wata mata ta laftawa mijinta tabarya akai ya mutu bisa zargin cin amanarta da matan banza da yake yi

Ji yanda wata mata ta laftawa mijinta tabarya akai ya mutu bisa zargin cin amanarta da matan banza da yake yi

Auratayya
Ana zargin Wata matar aure me suna Omolara Oluwakemi ta kashe mijinta, Seidu Jamiu ta hanyar lafta mai tabarya akai yayin da yake bacci bisa zargin yana cin amanarta. Lamarin ya farune a Akungba Akoko dake karamar hukumar Akoko North East dake jihar Onda a ranar 1 ga watan Yuni. Sun shekara 7 da yin aure kuma suna da yara 3. Wata majiya daga danginsu ta tabbatar da lamarin inda tace dama wannan rikici ya dade a tsakaninsu inda matar ke zargin mijin na cin amanarta. Saidai kakakin 'yansandan jihar, SP Funmilayo Odunlami-Omisanya ya tabbatar da faruwar lamarin saidai yace basu da tabbacin matar ce ta kashe mijin domin kuwa ita matar ce da kanta ta kai kara ofishinsu inda tace wani ya kashe mijinta. Yace dan haka zuwa yanzu basu kama kowa ba, suna bincike ne tukuna.
Hotuna: NLC ta kulle Asibitin Kano

Hotuna: NLC ta kulle Asibitin Kano

Siyasa
Marasa Lafiya na fama da kansu inda suka rasa madafa a asibitin Muhammadu Abudullahi Wase Teaching dake Kano saboda yanda ma'aikatan Asibitin suka ahiga yajin aikin NLC. Jaridar Daily Trust tace marasa lafiya da yawa da suka je ganin likita asibitin sun yi cirko-cirko saboda rashin likitoci. Wasu dole haka suka koma gida ba tare da sanin ranar da zasu sake komawa ganin likitan ba. Wata mata me fama da ciwon suga Binta Muhammad ta bayyana cewa, da tasan ba zata samu ganin likita ba da bata fito daga gida da wuri haka ba. Saidai wata majiya daga asibitin tace har yanzu ana kula da marasa lafiya wanda suke da matukar bukata. Bayan asibitin, Majalisar Jihar Kano, ofishin shugaban ma'aikata, babbar kotun jihar Kano, da kotun daukaka kara da sauran manyan ma'aikatu duk a kulle suk...
Kalli Bidiyo: NLC ta kulle jami’ar Kaduna Polytechnic

Kalli Bidiyo: NLC ta kulle jami’ar Kaduna Polytechnic

Kaduna
Kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Kaduna ta kulle jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna Polytechnic biyo bayan yajin aikin data fara a yau, Litinin na sai baba ta gani. NLC sun je reshen jami'ar dake Unguwan Rimi inda suka fitar da daliban dake ciki suka kulle makarantar, kamar yanda Channels TV ta ruwaito. https://twitter.com/channelstv/status/1797559071605653659?t=47Z-RGNiOLuG4lJF6Zot5Q&s=19 A Abuja ma dai haka lamarin yake inda NLC ta kulle guraren aiki da yawa ta hana ma'ikata shiga.
Da Duminsa: Babban Bankin Najeriya, CBN ya soke lasisin bankin Heritage Bank da kuma kulle bankin

Da Duminsa: Babban Bankin Najeriya, CBN ya soke lasisin bankin Heritage Bank da kuma kulle bankin

Siyasa
Babban bankin Najeriya, CBN ya sanar da soke lasisin bankin Heritage Bank da kuma kulle bankin. Babban Darakta a CBN, Hakama Sidi Ali, ne ya bayyana hakan inda yace an dauki wannan mataki ne dan tsaftace harkar banki da kuma karawa mutane kwarin gwiwar yadda da tsarin banki a kasarnan. Ya kara da cewa bankin na Heritage Bank ya kasa fitar da bayanai kan yanda yake gudanar da ayyukansa dan ganin ya ci riba ko ya fadi. Sannan an bashi damar farfadowa daga matsalar da yake ciki amma lokaci me tsawo ya wuce bankin bai nuna alamar farfadowa ba dan hakane CBN ta ga cewa kawai abu magi a'ala shine rufe bankin. CBN ta kara da cewa hukumar (NDIC) wadda ke baiwa kudaden Al'umma dake banki kariya ta hanyar Inshora ce zata kula da yadda za'a kulle bankin. CBN yace yana baiwa 'yan Najeri...
Ya kamata majalisa ta gaggauta sakawa kudirin dokar karin albashin ma’aikata hannu kamar yanda ta gagaguta sakawa kudirin dokar canja taken Najeriya hannu>>Femi Falana

Ya kamata majalisa ta gaggauta sakawa kudirin dokar karin albashin ma’aikata hannu kamar yanda ta gagaguta sakawa kudirin dokar canja taken Najeriya hannu>>Femi Falana

Siyasa
Babban lauya kuma me ikirarin kare hakkin bil'adama, Femi Falana ya nemi majalisar tarayya data gaggauta amincewa da kudirin dokar da zai karawa ma'aikata mafi karancin Albashi kamar yanda ta yi akan kudirin dokar canja taken Najeriya. Falana a wata sanarwa da ya fitar yace, tsohuwar dokar kudirin mafi karancin Albashi ta daina aiki dan haka akwai bukatar majalisar ta amince da sabuwar kudirin dokar. Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dai sun fara yajin aiki a yau, Litinin dan nuna kin amincewa da karin Naira dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi. Wannan kira na Femi Fala dai zai yiwa ma'aikata da yawa dadi ganin cewa hakan zai kawo fara biyan sabon mafi karancin Albashin da gaggawa.
Yajin Aikin NLC:Lamura sun tsaya jik a Abuja

Yajin Aikin NLC:Lamura sun tsaya jik a Abuja

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa tituna da ma'aikatu babu mutane sosai a Abuja saboda yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC ta tsunduma a yau, Litinin. Rahoton yace babbar kotun kasa, ma'aikatar mata ta tarayya, da sauransu duk an kulle saboda yajin aikin. Kungiyar NLC dai ta shiga yajin aikinne saboda nuna rashin jin dadin Naira dubu 60 da gwamnatin tarayya tace zata biyasu a matsayin mafi karancin Albashi.
Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?

Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?

Siyasa
Masana sun bayyana damuwa game da yawan bashin da gwamnatin tarayya ta ciwo a shekara daya data gabata. Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a hannun 'yan Najeriya. Hakan na nuna cewa, yawan bashin da gwamnatin Tinubu ta ciwo ya fi wanda Gwamnatin Buhari ta ciwo a shekararta ta karshe akan mulki da kaso 117. Masana sun bayyana damuwar cewa hakan zai iya kawo karuwar hauhawar farashin kayan abinci da kara kudin ruwa na karbar bashi.