Thursday, December 18
Shadow
Kalli Hoto: An dakatar da  Dan kwallo Kungiyar Monaco Mohamed Camara saboda yaki yadda yayi tallar Luwadi

Kalli Hoto: An dakatar da Dan kwallo Kungiyar Monaco Mohamed Camara saboda yaki yadda yayi tallar Luwadi

Duk Labarai
An dakatar da dan kwallon kungiyar Monaco Mohamed Camara Saboda yaki yadda yayi tallar Luwadi. An dai baiwa 'yan Kwallon kaya da tambarin Luwadi a jiki shine ya samu wani abu ya rufe nashi tambarin na luwadi dake jikin rigarsa. Dalilin hakane yasa aka dakatar dashi na tsawon wasanni 4. Camara wanda musulmi ne ya ki yadda yayi tallar luwadinne dan kare martabar addininsa.
Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Ahmad Jalam ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Misau-Darazo ranar Asabar a cewar gwamnatin jihar

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Ahmad Jalam ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Misau-Darazo ranar Asabar a cewar gwamnatin jihar

Siyasa, Sokoto
Gwamna Bala na Jihar Bauchi Ya Halarci Jana'izar Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Allah Ya Karɓi Rayuwarsa A Daren Jiya Gwamna Bala Mohammed ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Alh Ahmad Aliyu Jalam Kwamishinan ƙananan Hukumomi na jihar Bauchi wanda ya Rasu a sakamakon hatsarin Mota Daga Bauchi Zuwa Jalam Gwamna Bala Mohammed ya bayyana shi a matsayin abokin aiki mai himma da kwazo da bayar da gudunmawar ci gaban Gwamnatin PDP a Jihar Bauchi. Ya ƙara da cewa Rasuwar Ahmed Aliyu Jalam ta haifar da zullumi tare da yin zaman makoki, yana mai rokon Allah ya ba shi AlJannati Firdausi, ya kuma baiwa iyalansa kwarin guiwar jure wannan babban rashi. Sai dai ya jajantawa ‘yan uwa da al’ummar Jalam a madadin Gwamnatin jihar da jam’iyyar PDP da daukacin al’ummar jihar Bauchi. Manyan ja...
Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da suka yi wa ‘yan Nijeriya gargadi kar su sake yin kuskuren zaben jam’iyyar APC a zaben 2023

Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da suka yi wa ‘yan Nijeriya gargadi kar su sake yin kuskuren zaben jam’iyyar APC a zaben 2023

Siyasa
Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun gargaɗi ƴan Najeriya kan sake zaɓen APC a 2023. Tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana cewa halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan yanzu, kin ɗaukar shawara ne ya kawo shi. Tambuwal ya bayyana hakane a wajan wani taron maau ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar Sokoto. Yace sun gayawa mutane, APC mulki kawai take aon samu ta ganta a ofis. Yace gashi yanzu sun samu amma sun rasa yanda zasu yi dashi.
Hoto: Hazikin Dansanda ASP Usman Lawal Tangible Ya Rasu A Katsina

Hoto: Hazikin Dansanda ASP Usman Lawal Tangible Ya Rasu A Katsina

Katsina, Tsaro
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Hazikin Dansanda ASP Usman Lawal Tangible Ya Rasu A Katsina Allah Ya Yi Wa Hazikin Dansanda ASP Usman Lawal Tangible Rasuwa A Garin Malumfashi, Jihar Katsina Yau Lahadi. An Yi Jana'izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci A Gidansa Dake Bisije Babban Gida, Karamar Hukumar Malumfashi Jihar Katsina. Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Hotuna: Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Cafke Shahararren Dan TikTok Mai Rawa Da Mata Lawancy

Hotuna: Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Cafke Shahararren Dan TikTok Mai Rawa Da Mata Lawancy

Jaruman Tiktok, Nishadi
Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Cafke Shahararren Dan TikTok Mai Rawa Da Mata Lawancy. A ci gaba da sumamen tsaftace kafafen sada zumunta da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ke yi, ta cafke matashin nan Rabi'u Sulaiman da aka fi sani da Lawancy. Hisbah na zarginsa da ci gaba da raye-rayen baɗala da riƙe hannun mata a bidiyo. Idan za ku iya tunawa ko a shekarar 2023 ma Hisbah ta taɓa kama shi, amma ya nemi afuwa ya ce ya tuba.
Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Siyasa
Rahoton da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC zata ci gaba da yajin aikin da ta dauri aniya gobe, Litinin bayan zaman sulhu da gwamnati ya ci tura. A yau lahadi ne dai aka zauna tsakanin wakilan gwamnatin tarayya daga majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dan cimma matsaya kan mafi karancin Albashi, saidai an kare zaman ba tare da cimma matsaya ba. Da misalin karfe 5:50 PM ne dai aka fara zaman inda aka kareshi da misalin karfe 8:45 PM. Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio bayan taron, ya gayawa manema labarai cewa gwamnati ta roki kungiyoyin kwadagon kan su janye yajin aikin nasu amma suka kiya. Akpabio yace idan aka yi yajin aiki, abubuwa da yawa hadda asibitoci a kasarnan zasu tsaya cik. Duk da haka dai ya sake rokon kungiyoyin kwadagon da ...
A karshe dai, ba dan yana so ba, Shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da Tsagaita Wuta akan Falas-dinawa bayan Tursasawar kasar Amurka

A karshe dai, ba dan yana so ba, Shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da Tsagaita Wuta akan Falas-dinawa bayan Tursasawar kasar Amurka

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da tsagaita wuta akan Falas-dinawa bayan tursasawar kasar Amurka. Rahoton yace, Israela ta amince da tsagaita wutarne a Yau, Lahadi. A ranar Juma'ar data gabata ne dai Shugaba Biden ya gabatar da tsarin na tsagaita wuta wanda Benjamin Netanyahu yayi watsi dashi. Saidai a yau ya amince. Hakanan akwai rahotannin dake cewa, itama kungiyar Hamas ta amince da tsarin, amma bata sanar da hakan a hukumance ba. Me baiwa Benjamin Netanyahu shawara kan harkokin kasashen waje, Ophir Falk ne ya bayyana hakan inda yace ba shiri bane me kyau amma suna son kubutar da duka mutane su dake hannun Hamas shiyasa suka amince dashi. Saidai ya nanata aniyarsu ta son ganin bayan kungiyar ta Hamas.