Friday, December 5
Shadow

PDP ta koka da cewa, APC na ta mata kwacen mutanenta inda a yanzu haka Gwamnonin da suka rage ana musu Alkawari me gwabi idan suka shiga APC

Rahotanni sun bayyana cewa, jam’iyyar APC me mulki nawa gwamnonin PDP da tsaffin Gwamnonin jam’iyyar Alkawura masu gwabi idan suka yadda suka koma jam’iyyar.

Rahotanni daga Punchng sun ce APC nawa Gwamnoni masu ci alkawarin za’a basu tikitin sake tsayawa takara idan suka yadda suka koma jam’iyyar ba tare da abokin takara ba, sannan kuma za’a basu dama su zabi wanda zai gajesu da wadanda zasu tsaya takarar ‘yan majalisa.

Sannan tsaffin Gwamnonin dake cikin PDP ana musu Alkawarin za’a basu mukaman Minitoci.

Saidai Rahotan yace Atiku Abubakar yana jan hankalin su da cewa goyon bayan Tinubu kamar goyon bayan Rashin Nasara ne da Gwamnatin data gaza, inda yake jan hankalinsa da su goyi bayansa.

Karanta Wannan  Me ya sa gwamnatin Malaysia za ta hana amfani da motocin CNG?

Kakakin PDP, Debo Ologunagba ya koka da cewa, ana Amfani da Mulki wajan matsawa ‘yan jam’iyyar su komawa APC.

Saidai yace masu komawa APC din ba zasu tseratar da shugaba Tinubu ba daga fushin Al’umma ba.

Saidai a bangare guda kuma, Sakataren jam’iyyar APC Ajibola Basiru ya musanta wannan zargi inda yace mutane bisa radin kansu ne suke komawa APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *