Wednesday, April 1
Shadow

Rahotanni naa cewa akwai yiyuwar Rarara zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC

Wasu rahotanni dake yawo a kafafen sada zumunta sun bayyana cewa Tauraron mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara na shirin barin jam’iyyar APC zuwa ADC.

Rahoton yace abinda ya batawa Rarara rai har yake shirin barin jam’iyyar ta ADC shine rashin tafiyar da ba’a yi dashi ba zuwa kasar Ingila da shugaba Tinubu ya kai ziyara.

An dai hangi mawakiyar kudu, Tiwa Savage a cikin tawagar shugaba Tinubu a ziyarar da ya kai Ingilar inda aka rika cece-kuce cewa ba a dauki mawakin Arewa ko guda a cikin tafiyar ba.

Zuwa yanzu dai babu abinda Rarara yace akan lamarin.

Karanta Wannan  Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar yaƙi da miyagun ƙwàyòyì

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *