
Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry da ke unguwar Sabon Tasha a ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ya raba wa musulmi masu ƙananan ƙarfi da makarantun addinin musulunci kayan abinci domin su samu abin sakawa a bakin salati a lokacin azumi.
Shugaban coci, Fasto Yohanna Buru ne ya jagoranci raba kayan abincin, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin musulmi da kirista.
“Muna mayar da biki ne kan yadda Hajiya Ramatu Tijjani take yawan ba kirista kayan abinci a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara,” in ji shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Fasto Buru ya ce suna da burin tallafa wa aƙalla mutum 1,000 ne a azumin na bana, sannan ya ce ya jagoranci haɗa malamai da fastoci aƙalla guda 30 domin gangamin jawo hankalin ƴan kasuwa game da muhammancin rage farashin kayan abinci.