
Tsohon gwamnan jihar Imo, Achike Udenwa ya bayyana cewa lamarin siyasa da mulki a kasarnan ya tabarbare inda komai ya koma maganar kudi.
Yace idan kana da kudi, zaka iya saye Sojoji, ‘yansansa, Hukumar zabe dama masu zaben.
Ya bayyana hakane a wajan wata hira da aka yi dashi.
Yace yanzu idan mutum ya fito neman zabe babu maganar me zaiwa mutane ko menene halinsa, kudi kawai ake dubawa, kowa yana duba me zai samu.