Daga Shafin Dimokradiyya:
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokradiyya ta shekarar 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babbar sakatariya ta ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Aishetu Ndayako, ta fitar ranar Talata a Abuja.
Ndayako ta bayyana cewa ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar wannan rana.
Ya ce a yayin da al’ummar kasar ke bikin ranar dimokuradiyya a tarihinta, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi tunani a kan irin kokarin da iyayenmu suka yi wajen ganin Nijeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya.
Tunji-Ojo ya kara da cewa, ya kamata Najeriya ta kasance cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya ba tare da rabuwar kai ba domin amfanin kowa.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da dagewa kan tsarin mulkin dimokradiyya.
Ministan ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kawo sauyi mai kyau domin farfado da tattalin arzikin kasa da inganta tsaro.
Tunji-Ojo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da abokan Najeriya da su yaba da ci gaban da aka samu tare da fatan samun kyakkyawar makoma ga Dimokuradiyyar Najeriya.
Ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan murnar zagayowar ranar dimokuradiyya.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar 7 ga watan Yunin shekarar 2018, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin cewa daga yanzu za a gudanar da ranar dimokuradiyyar kasa a ranar 12 ga watan Yuni na kowace shekara sabanin yadda ake gudanar da bikin a ranar 29 ga watan Mayun kowacce shekara.
Buhari ya kuma karrama wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka soke ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, Cif Moshood Abiola, da babbar lambar girmamawa ta kasa, Babban Kwamandan Tarayyar Najeriya.
Buhari ya ci gaba da cewa, zaben ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, shi ne zabe mafi inganci, gaskiya da lumana tun bayan samun ‘yancin kai.
“Ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, ita ce ranar da miliyoyin ‘yan Nijeriya suka bayyana ra’ayinsu na Dimokuradiyya a zabuka mafi inganci, gaskiya da lumana tun bayan samun ‘yancin kai. Cewa sakamakon zaben da gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin ba ta amince da shi ba, hakan ba zai sa ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dimokradiyya,” inji shi.
Shugaba Buhari ya kuma ba Baba Gana Kingibe lambar yabo ta kasa tare da karrama marigayi Gani Fawehinmi bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da zaben ranar 12 ga watan Yuni.
Abiola dai ya mutu ne a tsare yayin da yake fafutukar ganin ya cika aikin sa kamar yadda ya kunsa a zaben da aka soke.
Daga: Abbas Yakubu Yaura