
Rahotannin da Hutudole ke samu na cewa, Rarara da Rashida Mai Sa’a sun sa an saki hassan Make-Up daga ofishin ‘yansanda bayan kamun da aka masa.
Hutudole ya fahimci cewa da misalin karfe 10 na dare ne aka kama Hassan Make-Up inda ya kwana a ofishin ‘yansandan.
Sannan da Misalin karfe 10 na safe aka sakeshi.
Rahotanni sun ce Hassan Make-Up ya zo Najeriya ne halartar bikin Rarara da kuma yiwa Mai Wushirya gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa.
A wani Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sadarwa, An ga yanda wani dansanda ya mari hassa Make-Up tare da zaginsa wana haka ya sabawa aikin dansanda.