Tuesday, May 6
Shadow

Rashin tsaro da kashe-kashe sun ragu da kashi 90% a Najeriya, in ji NSA, Ribadu

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Najeriya ta samu raguwar rashin tsaro da kashe-kashe da kusan kashi 90 a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Ribadu ya bayyana haka ne a garin Jos na jihar Filato a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Janar Folusho Oyinlola a ofishinsa, biyo bayan harin da yan indiga suka kai kan al’ummar Bokkos wanda ya yi sanadin mutuwar mazauna garin da dama.

A cewarsa, gwamnatin shugaba Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Karanta Wannan  Matsalolin Nijeriya Na Bukatar A Yi Musu Taron-Dangi Domin Ganin An Yaki Talaùcin Da Ya Addabi Al'ummar Kasar, Inji Kashim Shettima

“A cikin shekaru 1-10 da suka wuce, an rage yawan da kusan kashi 90 cikin 100 a kasarmu.

“Muna da kididdigar ta shekarar 2022 da 2023, inda aka nuna cewa wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon mummunan tashin hankali a kasar nan sun ragu,” Mista Ribadu ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *