
Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya gargadi ‘yan Najeriya da cewa, kada wanda ya sake baiwa masu garkuwa da mutane kudin fansa.
Ya bayyana hakane a Kaduna yayin da yake karbar wasu da aka yi garkuwa dasu amma jami’an tsaro suka kubutar dasu mutane 60.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, biyan masu garkuwa da mutanen kudin fansa yana kara karfafa musu gwiwa kuma hakanne zai sa su ci gaba da neman kudin fansar.
Yace Gwamnati na iya bakin kokarinta na ganin ta bisu har maboyarsu ta yi maganinsu.