Saturday, May 24
Shadow

Rikicin Aminu J Twon, Ordinary President da matar soja, Waye me gaskiya?

Matar soja Seaman Haruna Abbas ta dauki zafi sosai akan neman taimakon da Aminu J. Town yace ya mata inda ta yi ikirarin cewa ba da saninta bane.

Hakanan Shima Ordinary President, Ahmad Isah wanda ta je gidan talabijin da rediyonsa wajan neman hakkin mijinta, ya dauki zafi duk da dai yawa Aminu J. Town Nasiha.

Hakanan a bangaren Aminu J. Town, shima bai dauki abin da sauki ba inda yayi zargin cewa ana son bata masa suna.

Aminu J. Town dai ya bayyana cewa an nemi ya tarawa matar sojan ruwa, Seaman Haruna Abbas wadda ta kai kara gidan talabijin na Ordinary president inda tace an tsareshi tsawon shekaru 6 ba tare da hukunci ba kan zargin yayi yunkurin kashe ogansa.

Karanta Wannan  An bayyana abu daya da ya ragewa Atiku da Peter Obi su yi idan suna son kayar da Tinubu a zaben 2027

J Town yace yayi kokarin neman lambar matar inda ya kira dan neman izinin tara mata taimakon.

Ga bidiyon wayar da Ordinary president yayi da Aminu J. Town:

Saidai daga baya matar tace da wayarta yayi amfani amma ba da ita yayi magana ba, J. Town ya nemi ta gaya masa da wa yayi magana amma matar tace ba zata fada ba.

https://www.tiktok.com/@dan_gaya2/video/7415365371621854470?_t=8pqeaheDtEE&_r=1

Hakan ya batawa J. Town rai inda ya zargi Ordinary president, Ahmad Isa da yin wata kullalliya akan lamarin.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Shugaban Nigeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Rome, Italy domin halartar bikin rantsar da sabon Paparoma Pope Leo XIV a ranar Lahadi mai zuwa

Lamarin dai tsakanin mutanen 3 ya rincabe inda Matar tace da wayarta J Town yayi magana amma ba ita ta yi magana dashi ba akan ya nema mata taimako ba kuma ba zata fadi wadda ta yi magana da J. Town din ba

A karshe dai an ga matar tana tofin Allah tsine ga J. Town bisa zargin yayi amfani da sunanta ya tara kudi inda kuma takewa Fauziyya D. Sulaiman ta Arewa24 godiya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, Fauziyya D. Sulaiman ta tarawa matar sojan ruwan Naira Miliyan 2.1 kuma Ordinary president ya amince da wannan tallafin kudi.

A wannan rikicin dai, ra’ayoyin mutane ya banbanta.

Karanta Wannan  Sanata Natasha ta taba bani labari game da haduwarta da Sanata Akpabio a dakin Otal, saidai na mata gyara inda nace mata a ofis ake haduwa a yi aiki ba a otal ba>>Sanata Kingibe

Inda wasu suka goyi bayan bangaren Aminu J. Town wasu kuma suka goyi bayan bangaren Ordinary president da matar soja.

Wasu sun yi zargin cewa Ordinary president ne ya tirsasawa matar sojan kin amincewa da maganar nema mata tallafi da Aminu J. Town yayi, ita kuma ganin tana karkashin gidan talabijin dinsa ne kuma ta nan ne zai nema mata taimako yasa ta amince da duk sharadinsa.

Masu shashi sun ci gaba da cewa Ahmad Isa na kokarin ganin ya yi amfani da wannan magana ta matar soja wajan kara samarwa gidan talabijin dinsa farin jini.

Saidai wasu na ganin Ahmad Isa din ya wuce da haka, Asalima ba sa’an yin Aminu J. Town bane.

Wasu masu sharhin na ganin cewa, maganganun da Aminu J. Town yayi na rashin kunyane ga Ordinary president wanda basu kamata ba saboda ba sa’an yinsa bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *