Friday, December 5
Shadow

Sabon Rahoto Da Duminsa:Rashin Lafiyar Shugaba Buhari ta yi tsanani

Ƴan Najeriya sun wayi gari da rahotannin da ke cewa an garzaya da tsohon shugaban Najeriyar, Muhamamdu Buhari zuwa wani asibiti a birnin London da ke Burtaniya.

An dai kwana biyu ba a ji ɗuriyar tsohon shugaban ba tun bayan komawarsa birnin Kaduna da zaman bayan kwashe kimanin shekaru biyu a mahaifarsa ta Daura bayan saukarsa daga Mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

BBC ta nemi jin ta bakin Malam Garba Shehu, tsohon maitaimaka wa Muhammadu Buhari a fannin yaɗa labarai.

Malam Garba Shehu ya ce Buhari ya tafi Burtaniya ne domin duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, amma daga baya sai ya kamu da rashin lafiya.

Karanta Wannan  Labarin Zuciya, A Tambayi Fuska: Ko dai Bata so ne?

“Ina so in tabbatar muku cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na rashin lafiya. Yana samun magani a Birtaniya.

“Idan kuka tuna, Buhari ya sanar da kowa cewa zai je duba lafiyarsa na shekara-shekara. Ya kamu da rashin lafiya ne a can, amma ina farin cikin sanar da ku cewa yana samun sauƙi a yayin da ake ci gaba da jinyarsa.”. In ji Garba Shehu.

Ya ƙara da cewa, “Muna addu’ar Allah ya ba shi cikakkiyar lafiya.”

Sai dai kuma Garba Shehu bai bayyana irin rashin lafiyar da Buhari ke fama da ita ba ko sunan asibitin da yake jinya a ciki ba.

To amma rahotanni na rawaito wasu majiyoyi daga makusanta da iyalan tsohon shugaban cewa yana sashen kualawa da marasa na musamman bisa fuskantar rashin lafiya mai tsanani.

Karanta Wannan  Da Duminsa: An yi gàrkùwà da dansandan Najeriya a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *