
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa ya karbi mulki Najeriya na daf da talaucewa.
Ya bayyana hakane a kasar Saint Lucia a yayin ganawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar.
Shugaba Tinubu yace amma yanzu Najeriya ta dawo hayyacinta anata walwala.
Yace sun dauki matakan gyara sosai wanda suka dora kasar kan Turbar ci gaba.