
Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua wanda ya wakilci mazabar Katsina ta tsakiya a majalisar tarayya ya bayyana cewa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
A takardar da ya aikewa da mazabarsa ranar 28 ga watan Yuli, Tsohon Dan majalisar ya bayyana cewa, tsare-tsaren jam’iyyar APC sun jefa al’umma cikin halin kaka nika yi.
Yace da gaskene kalaman Malam Nasir El-Rufa’i da yace gwamnatin Tinubu ta koma ‘yan Bindigar birni.
Abubakar Sadiq ‘Yar’Adua wanda yayi takarar gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 yace Gwamnatin Tinubu na biyewa Turawa ne wanda burinsu tara Duniya yana jefa ‘yan Najeriya a wahala.
Yace yana fatan shi da mabiyansa zasu koma jam’iyyar ADC nan gaba kadan